Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-Ahed cewa, mafi akasarin shirye-shiryen tarbar masu ziyara Arbaeen na Imam Husaini na kasar Iraki sun fi mayar da hankali ne kan shirye-shiryen hidima da suka hada da samar da ruwa da abinci da ayyukan kiwon lafiya da dai sauransu.
Dangane da haka ne a jiya aka gudanar da taron tuntuba na wakilai da jami'an kula da haramin kasar Iraki a birnin Najaf, kuma a cikin wannan taron an tattauna hanyoyin samar da ingantacciyar hidima ga masu ziyara a yayin gudanar da tarukan Arbaeen Husaini.
Salim Al-Jasani, memba a majalisar gudanarwa ta hubbaren Alawi, ya ce: "Ana sa ran cewa bayan guguwar corona ta lafa, za mu shaida kasancewar miliyoyin masu ziyara a taron Arbaeen na bana."
Har ila yau, domin yi wa masu ziyara hidima, an aiwatar da shirye-shirye da ayyukan hidima da dama a garuruwa daban-daban na kasar Iraki, wadanda suka hada da kayan aiki, da shiryawa da kuma shimfidu da katifu.